EDITA.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da gazawar tsarin gwamnati kan badakalar PFIPC, yana mai cewa bayanin da Fadar Shugaban Ƙasa ta bayar ya ƙara jefa shakku kan yadda hukumomin gwamnati ke aiki.
Atiku ya ce ba zai yiwu mutum ɗaya ya ƙirƙiri hukumar bogi, ya buɗe ofis a Sakatariyar Tarayya, ya gudanar da harkokinta tare da mu’amala da jami’an gwamnati ba tare da taimakon wasu ba. Ya kuma buƙaci CBN da EFCC su yi cikakken bayani kan lamarin.
Ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a badakalar, ba tare da la’akari da matsayinsa ko alaƙarsa da gwamnati ba.
Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta cewa PFIPC hukuma ce ta gwamnatin tarayya, tana mai cewa wanda ake zargi ya aikata hakan ne ba tare da izinin gwamnati ba.










