Daga Hassan R Jibrin.

Kungiyar Tsoffin Daliban Makarantar Sakandaren Gwamnati dake garin Ringim, aji na 1983, ta sanar da dage takunkumi akan daya daga cikin mambobinta, Alhaji Isah Usman Maimota.

A kwanakin baya ne wata takardama ta kaure kan wata makala da Maimota ya wallafa a shafin Kungiyar mai nasaba da wani dan kungiyar, a inda ce-ce-ku-ce ya barke a tsakanin mambobi.

Shugaban Kungiyar, Alhaji Auwalu Soja Bakin Wapa, ya sanar da dage takunkumin , bayan wata ganawa da iyalan wanda aka dakatar.

Bayan sanarwar, mambobin Kungiyar sun yaba da sabon matakin domin cigaba da kasancewa aminan juna masu dogon tarihin da ba zai taba goguwa ba.

Mai sa ido akan shafin kuma guda daga cikin Shugabannin Kungiyar,, Malam Suleiman Gambo.

Chai-chai, ya tabbatar da sake dawo da sunan Alhaji Isah Usman Maimota kan shafin Kungiyar.Wannan shine karo na farko da Kungiyar ta taba fuskanta har ta kai da sa takunkumi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here