Daga Hassan R Jibrin.
Mashawarcin Shugaba Bola Tinubu Kan Yada Labarai Da Tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar da wata sanarwa a shafin sa na Facebook, inda ya musanta batun sauyawa Najeriya suna zuwa Hadakar Jihohin Najeriya wato United States of Nigeria ,cewar zuki ta malle ce.
Fadar ta kuma kara da cewar gyaran tsarin mulkin kasa ba abu ne da Fadar za ta iya yi a cikin ruwan sanyi, domin sai Majilsar Dokoki ta samu kason biyu daga cikin uku na ilahirin mambobin haka kuma dole ne jihohi ashirin da hudu na Kasar sun amince ballantana soke tsarin shariyar Addinin Musulinci inda yafi karfi a mafi rinjayen Jihohin arewacin Kasar
Sanarwar ta kuma kara da cewar labarin da ake bazawa kanzon kurege ne maras tushe bare makama.
Ana zargin gwamnati da shirin ne ta mikawa Majalisun Dokokin Kasar wani daftari a ranar 15 ga watan Disamba ganin shine aikin Majalisun da zai zama na karshe a jumhuriya ta goma.










