Guarantee Newspaper.
Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa ya karbi matakin gwamnatin Kano na hana shi hawan sallah da ta yi domin zaman lafiya a Kano.
” Mun hakura , ba za mu yi Hawa ba kamar yadda gwamnati ta bada umarni saboda mu masu son zaman lafiya ne, ba maeu son duk wani abun da zai kawo wa jihar Kano rashin zaman lafiya ba”.
Alh. Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne ta bakin Hon. Aminu Babba Danagundi yayin wata ganawa da yayi da manema labarai.
Ya ce Sarki Aminu ya ba su umarnin su bi umarnin gwamnatin jihar Kano, don haka sun warware duk wani shiri da suka yi na gudanar da hawan sallar.
Babba Dan agundi ya yaba wa gwamnatin Kano bisa matakin da ta dauka, sai dai ya ga baiken gwamnatin na baiwa Sarki Sanusi damar yin hawan.
”Abun da gwamnatin kano ta yi na nuna cewa ta Amince Sanusi shi ne Sarki kuskure ne, domin haka ya sabawa doka tunda batun yana gaban kotu”. Inji Aminu Babba










