EDITA.

Shahararren ɗan kasuwa kuma hamshaƙin mai zuba jari a fannin man fetur da kadarori a Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Audu Manager, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 68 a duniya.

Ɗansa, Surajo Audu Manager, ne ya tabbatar da rasuwar tasa, inda ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Laraba a Asibitin Saudi German da ke birnin Alkahira na ƙasar Masar, bayan ya shafe wani lokaci yana jinya.

Marigayi Audu Manager ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan kasuwa a Kano da ma Arewacin Najeriya baki ɗaya, inda ya yi suna a harkokin kasuwancin man fetur tare da zuba jari a fannin gine-gine da bunƙasa kadarori.

Rasuwarsa ta girgiza al’ummar Kano da sauran sassan ƙasar, musamman abokan hulɗarsa da ‘yan kasuwa, yayin da ake ci gaba da karɓar saƙonnin ta’aziyya da addu’o’i daga mutane da ƙungiyoyi daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here