Daga Hassan R. Jibrin.
Karkashin Kungiyarsu, Gwamnonin Arewa, sun samar da Asusun Amintattu kan harkar tsaro a fadin yankin, karkashin jagoranci tsohon ministan tsaro kuma babban hafsan hafsoshin rundunar dakarun Najeriya, Martin Luther Agwai., yayin da tsohon Shugaban Ma’aikatan Tarayya Alhaji Mahmud Yayale Ahmed zai dafa masa.
Mambobin Asusun sun hada da DIG Rtd Hafiz Inuwa Ringim (Jigawa), Rtd Laftanar Janar Faruk Yahaya (Sokoto), Rtd IGP Usman Alkali Baba (Yobe), Boss Mustapha (Adamawa), Sanata Napoleon Bali Rtd AVM (Plateau), Rtd AVM Kabiru Aliyu (Taraba), Farfesa Usman Tar (Borno), Manjo Janar AM Dikko (Neja) da Rtd AIG Sunday Babaji (Gombe).
Sauran sune Rtd AVM Faruk Omeizi Umar (Kogi), Manjo Janar Muhammed Sani (Kano), Manjo Janar Bello Sarkin Yaki (Kebbi), Manjo Janar John Malu (Benue) sai Birgediya Janar Ibrahim Agbab (Kwara).
Kudaden gudanar da Asusun za su dogara ne daga Asusun Kananan Hukummomin jihohin yankin na Arewa, inda naira biliyan daya a duk wata za’a zabtaro har na tsawon shekara daya.
Shi dai wannan Asusun Amintattu,an dora masa alhakin tsarawa da gudanar da harkokin tsaro mai dorewa ta hanyar aiki kafada da kafada da bangarorin tsaro da ke gudanar da aiyukansu a ilahirin fadin yankin na Arewa.
Kafuwar wannan Asusu ka iya fitar da A’i daga Rogo, domin mafi yawa daga cikin mambobin sun yi shura a fannin tsaro da hatkar gudanar da tsare-tsare.










