Daga Wakilin Mu.

Ɗan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Sanata Sabo Mohammed Nakudu, CON, a ranar Lahadi ya fara fitowar sa ta farko a bainar jama’a tare da abokin takararsa na neman kujerar mataimakin gwamna a zaɓen 2027, Alhaji Aminu Ibrahim Ringim, bayan naɗa shi a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar.

DfWannan ziyara ta farko da ‘yan takarar suka gudanar tare, wadda ta ja hankalin ‘ya’yan jam’iyya da masu bibiyar harkokin siyasa, ta ƙunshi jerin ziyarce-ziyarce na ta’aziyya da nuna jaje a sassa daban-daban na Ƙaramar Hukumar Dutse, abin da ke nuna aniyar haɗin guiwar ‘yan takarar wajen kusantar jama’a da ƙarfafa alaƙa da al’umma.

Tawagar ta fara gudanar da ayyukanta ne da kai ziyarar ta’aziyya ga wani dattijon jam’iyyar ADC, Alhaji Uba Maranjuwa, bisa rasuwar ɗan uwansa.

Daga nan tawagar ta zarce zuwa wajen Alhaji Aminu Nuhu Jahun domin duba lafiyarsa tare da yi masa fatan samun cikakkiyar lafiya bayan rashin lafiyar da ya yi fama da ita a baya-bayan nan.

Daga bisani ɗan takarar gwamna da mataimakinsa sun wuce garin Chaichai, inda suka kai ziyara ga iyalan marigayi Ibrahim Baba Chaichai domin jajantawa bisa rasuwar ɗan uwansa, tare da yi wa mamacin addu’ar Allah Ya gafarta masa, sannan Ya bai wa iyalansa haƙurin jure wannan rashi.

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana waɗannan ziyarce-ziyarcen a matsayin fitowar jama’a ta farko da aka haɗa tare tsakanin Sanata Nakudu da Alhaji Ringim tun bayan sanar da naɗin Alhaji Ringim a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna na ADC, suna masu cewa wannan mataki ya nuna muhimmancin da jam’iyyar ke bai wa tausayi, taimakon juna, kusantar jama’a da ƙarfafa gwiwar magoya bayanta na ƙasa.

Bayan kammala ziyarce-ziyarcen da suka gudanar a Dutse, Alhaji Aminu Ibrahim Ringim ya koma garinsu na Ringim, inda ya ci gaba da karɓar dimbin shugabannin jam’iyya, magoya baya, abokan hulɗa da masu taya shi murna bisa samun nasarar zama abokin takarar Sanata Sabo Nakudu.

A halin da ake ciki, wasu masu ruwa da tsaki da magoya bayan ADC sun bayyana kwarin gwiwarsu kan haɗin gwiwar takarar gwamna na jam’iyyar, inda suka bayyana haɗin Sanata Nakudu da Alhaji Aminu Ringim a matsayin ƙawance mai ƙarfi da ya ƙunshi gogewa, karɓuwa a tsakanin jama’a tun daga tushe na siyasa wanda shi ake buƙata domin gudanar da gasa mai ƙarfi a zaɓen gwamna na 2027.

Masu ruwa da tsakin sun bayyana cewa ci gaba da wayar da kan jama’a a matakin tushe, kyakkyawan tsari na yaƙin neman zaɓe da kuma goyon bayan masu zaɓe, takarar Sanata Sabo Mohammed Nakudu da Alhaji Aminu Ibrahim Ringim zata kasance cikin kyakkyawan matsayi na yin gasa mai ƙarfi domin samun nasara a zaɓen gwamnan Jihar Jigawa na shekarar 2027, in Allah Ya yarda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here