Hassan Turaki.
Innalillahi wa’inna ilaihir-raji’un
Mun samu labarin rasuwar Dr. Ahmad Ibrahim Bauchi, mataimakin daraktan ilimi a Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) na jihar Bauchi.
Malam Ya rasu ne bayan yayi gajeriyar rashin lafiya, tuni dai akayi masa janaiza jiya Lahadi, 19 ga watan Yuli na shekarar 2026 da ƙarfe 1:00 na rana.
Muna jaddada du’a’in ALLAH yayi masa rahama yasa aljannah firdausy ce makomar sa. Idan tamu tazo yasa mu cika da imani.










