Daga Hassan R. Jibrin.
Hukumar shirya jarrabawa ta Kasashen Afirka ta Yamma (WEAC), ta sanar da rike wasu sakamakon Jarrabawa da Hukumar ta shirya a wannan shekarar, har guda 167,486, wanda ke wakiltar kaso 8.59 cikin dari na wadanda suka zauna rubuta Jarrabawar kammala karatun sakandare a Kasashen na Afirka ta Yamma, wanda akayi ta hanyar na’ura mai kwakwalwa.
Rike sakamakon ya biyo bayan zargin magudi, duk da cewar an samu raguwar adadin akan shekarar 2025, inda alkaluman ke nuni da kaso 9.7 a cikin dari.
Sanarwar ta fito ne daga bakin Shugaban Ofishin na Najeriya, Dr Amos Dangut, yayin jawabin sakin sakamakon Jarrabawar da ya gudana a Ofishin dake Legas.
Dr Dangut yace an rike sakamakon wadanda abin ya shafa ne saboda mabambantan dalilan da suka hada da, karuwar amfani da wayar hannu duk da haramcin dake akwai, sannan da shirya magudi a tare a wasu Makarantu.










