Daga Musa Muhammad Hadejia.
Al’ummar yankin Garin Jiyan da ke karamar hukumar kirikasamma sun yabawa Gwamnatin jihar Jigawa busa Fara aikin Jinga a yankin domin samun kariya daga ambaliyar kogi.
Mai bawa Gwamna shawara akan shigo da al’ummah cikin Gwamnati da Kuma daukar matakan kariya daga ambaliyar kogi Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya bayyana hakan ga manema labarai yayin Gudanar da aikin.
Alhaji Hamza yace aikin jingar gabar kogin na daya daga cikin aiyukan Gwamnatin jihar Jigawa wajen kare dukiyoyin al’ummah daga ambaliyar kogi.
Ya Kara da cewa ta shirya tsaf domin daukar matakan gaggawa wajen ganin Gonakin manoma da Kuma matsugunnan da ke kusa da gabar kogi sun samu kariya domin inganta aiyukan noma a fadin jihar Nan.
Daya daga cikin mazauna Garin na Jiyan da ke karamar hukumar kirikasamma Malam Wakili Hamza Jiyan ya nuna godiyar sa busa aikin Jingar gabar kogin domin manoma daga ifatala’in ambaliyar kogi.
Ya Kara da cewa a shirye suke su bada dukkan gudun mawa domin ganin Gwamnatin Malam Umar Namadi ta cigaba d mulki har zuwa shekara ta 2027 domin cigaba da sharfar romon damokaradiyya.










