Daga Hassan R. Jibrin.

Tsohon Shugaban jam’iyyar APC na Kasa kuma tsohon Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yayi karin haske akan gaida Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, alokacin bikin nadin mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Murtala Sule Garo.

Ayayin bikin, aka jiyo tsohon gwamnan na kwatanta Sarkin da”Maimartaba kuma shugaban majalisar sarakuna”Kakakin tsohon gwamnan Kwamred Muhsmmed Garba, ya sanar da cewa, wannan gaisuwar ba tana nufin yin muba’aya, sai dai tsarin taro ne kuma baya goyon bayan wani mai neman sarauta Kotun Koli ce za ta tabbatar da hakan”.Rikicin masarautar Kano, ta dade a gaban Kotu domin neman warware matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here