Daga Hassan R Jibrin.
Cikin shirye-shiryen gudanar da bikin shigowar watan Rabi’ul Awwal, Kungiyar Shu’ara’u ta Kasa reshen jihar Kano, ta gudanar da addu’o’in na musamman kan cika shekara daya da rasuwar Mataimakin Shugabanta na jiha, marigayi Abdullahi Shehu Dangano.
A yayin addu’ar ne, tsohon wakilin Dawakin-Kudu/ Warawa, a Majalisar Dokokin Tarayya, Hon Mustapha Bala Dawaki, ya kara nuna alhininsa ga babban gibin da Kungiyar ta samu a fannin begen fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).
“Babu shakka, za’a dau dogon lokaci kafin cike gurbin da marigayi, Abdullahi Shehu ya bari.Da fatan ganin Halifansa ka iya kaiwa” a cewar Hon Bala Dawaki.
Mawallafa kasidun begen Annabi (SAW) sama da 500 ne suka yiwa garin na Gano cikar kwari daga sassa daban-daban.
Hon Mustapha, ya kuma yi addu’ar neman gafarar Allah(SWT) ga marigayin,da kuma rokon Allah ya albarkaci zuriyar da ya bari.
Manyan malamai daga dariku mabanbanta ne suka jagoranci gudanarwar da addu’o’in karkashin jagorancin Sheik Al-Bashir bn Ilyas bn Abbas.










