Hassan R Jibrin.
Biyo bayan wani umarnin Kotu da Hukumar Hana Almundaha da Zanba EFFC, ta nema domin toshe asusun jihar Osun kan zargin zambar kuɗade na dubban miliyoyi, dab da zaben gwamna da ake shirin gudanarwa.
Shugaban Kasar, ya nuna bacin ran sa kan abun da Hukumar tayi.
Ya kuma bada unarnin ga Hukumar ta koma Kotun domin janye Umarnin. Shugaban yanuna cewar Unarnin ya zo ne a yanayin da bai dace ba.
“Al’umma za su yi zargin da sa hannuna ko masaniyata, hakan ba dai-dai ba ne” acewar Shugaban.
Kafin wanna umarnin na Shugaban Kasar, jam’iyyu adawa na kallon Fadar Shugaban da bullo da wani sabon salon magudin zabe da kuma da yunkurin murkushe ‘yan adawa.
Wasu na ganin, ziyarar da kwamatin manyan Limaman Kiristoci bisa jagoranci Rebaren Onayeakan, ya taimaka wajen saita Shugaban kan sakarwa ‘ysn adawa mara domin tabbatuwar mulkin dimokaradiyya, a inda Kasar aka zurawa idanu daga sauran kasashen duniya da kungiyoyin dake rajin kare tsarin na dimokaradiyya.










