Daga Hassan R. Jibrin.
Allah ya yiwa tsohuwar shugabar matan jam’iyyar APCn jihar Kano, Hajiya Habiba ‘Yandalla rasuwa.
Marigayiyar mai shekaru kusan hamsin da biyu, ta jagoranci matan APC daga 2015 zuwa 2019.
Alokacin rayuwarta, ta taka gagarumar rawa wajen ganin ana damawa da mata a fannoni daban-daban.
Marigayiyar ‘yar asalin Karamar Hukumar Warawa ce daga kauyen ‘Yandalla.
Wasu na ganin cewa za’a dinga tunawa da ita wajen gudunmawar ta da yunkurin kyautatawa mata da yara kananan. Allah ya jikanta. Ameen










