DAGA WAKILIN MU.

An shirya wani taro a garin Kiru da ke Jihar Kano domin ƙona hular Kwankwasiyya.

Wannan na zuwa ne a matsayin mayar da martani ga zargin cewa wasu magoya bayan Kwankwasiyya sun ƙone hular Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da ta Gwamna Abba Kabir Yusuf, me dauke da alamar jam’iyyar APC.

Cikin wani rahoto da Siyasarmu TV ta fitar, an ce taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin ɗan Majalissar Tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa.

Jagororin jam’iyyar APC da sauran masu fada a ji sun halarci taron domin nuna goyon bayan su ga Shugaban Ƙasa, Gwamna da jam’iyyar APC.

An bayyana cewa abin da ya jawo wannan taro shi ne wani lamari da aka ruwaito jagoran Kwankwasiyya na yankin Kiru, Bello Shahus, ya jagoranta, inda aka ƙone hular Tinubu da ta Gwamna Abba.

A lokacin taron, magoya bayan APC sun bayyana bacin ran su kan lamarin, inda suka ce za su tsaya wajen kare mutuncin shugabannin su da jam’iyyar APC a kowani mataki.

Sun kuma yi kira ga ’yan siyasa da magoya bayan jam’iyyu da su nisanci duk wani aiki da zai iya haddasa tashin hankali ko rusa zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here