Hassan Turaki.
An gudanar da babban taron buɗe shagon aikin na’ura mai kwakwalwa mai suna ABSAF Cafe a kan titin Hakimi dake birnin Dutse, wanda ya samu halartar manyan yan kasuwa, abokan hulɗa da sauran al’umma daga sassa daban-daban.
Taron ya samu halartar masu jawabi wajen tattauna kalubalen da matasa ke fuskanta a fagen kasuwanci da kuma hanyoyin inganta su.
Da yake jawabi a wajen taron, Malam Ibrahim Me Gausu ya ja hankalin iyayen gida kan rashin adalci da wasu ke yiwa yaran su a harkar kasuwanci.
Ya ce, “Yara da yawa suna shan wahala a wajen iyayen gida ba tare da an basu kuɗin da ya dace ba, ko kuma ba’a taimaka musu su tsaya da kafafun su ta hanyar buɗe musu nasu kasuwancin ba”.
Me Gausu ya bukaci al’umma su ba matasa kyakkyawar horo da dama domin su zama masu dogaro da kansu.
Shima Malam Umar Abubakar Ladan yayi kira ga matasa da su dage wajen neman abin dogaro da kansu.
Ya tunadar da al’uma cewa addinin Musulunci ya karfafa neman arziki mai albarka maimakon zaman kashe wando.
Ladan ya kuma shawarci sabon ɗan kasuwa, Abubakar, da ya riƙe aikin sa da amana, ya guji haramci, domin hakan shine ginshiƙin samun albarka a kasuwanci.
A nasa jawabin, Malam Usama Adamu ya bayyana farin cikin sa da wannan cigaba da Abubakar ya samu.
Ya jaddada cewa gaskiya da rikon amana sune makullin ci gaban kowace harka ta kasuwanci.
Haka zalika, Malam Murtala ya ja kunnen Abubakar da ya ci gaba da riƙon amana kamar yadda ya saba.
Da yake jawabin godiya, mai shagon *ABSAF Cafe*, Abubakar Garba Isma’il wanda aka fi sani da “Computer Gurru”, ya nuna godiyar sa ga dukkan mahalarta taron bisa karɓar gayyata da kuma shawarwari masu amfani da suka ba shi.
Ya yi alƙawarin zaman lafiya da al’ummar yankin Hakimi Street da kuma ci gaba da riƙon zumunci.
Makusanta da abokan ciniki da dama sun halarci taron, inda suka yaba da ƙoƙarin Abubakar na buɗe wannan katafaren shagon na’ura mai kwakwalwa, suna mai fatan samun nasara da albarka a cikin harkar sa.










