Hassan Turaki.
Kamar yadda jadawalin zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC ya tabbatar, jam’iyyar ta gudanar da zababbukan ta na fidda gwani a kowacce karamar hukumar jihar Jigawa kamar yadda ta kasance a sauran jihohin Nigeria.
Kujerun da aka gudanar da zababbukan sun hadar da Kujerar takaran Shugaban Kasa inda jam’iyyar take da yan takara Uku. Yan takaran sun hada da:
Atiku Abubakar
Rotimi amaechi
Muhammad Hayatudeen
Ya zuwa yanzu an samu sakamakon zaben daga jihohi da dama na fadin Kasar nan.A nan jihar Jigawa ana cigaba da tattara sakamakon zaben yayin da al’uma ke jiran gwarzon Dan takaran gwamna da za’a fafata da shi a matakin shugabancin kasa da gwamnan jihar Jigawa dama kujerun majalissar tarayyar kasa.










