Daga Hassan R Jibrin

Shugaban Ma’aikatan Ofishin Shugabanin Jam’iyyar APC na Kasa, Honarabul Mustapha Bala Dawaki, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NDC.

Ficewar ta sa ta biyo bayan nuna rashin gamsuwa da rawar da gwamnatin jiha ta taka wajen zaben fidda gwani da kuma rashin baiwa tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar APC damar taka rawar nema mata nasara a zaben 2027.

Wasu na ganin abin boye ne ke fitowa fili a sannu, dangane da irin gashin kumar da bangaren gwamnati ke nunawa tsoffin ‘ya’yan jam’iyyar.

Ficewar ta Honarabul Bala Dawaki wata koma baya ce ga APCn Kano ganin dunbin magoya baya da kuma ingantattun ayyukan raya kasa da ya aiwatar a tsakanin 2011 zuwa 2023, a matsayin wakilin kananan hukummomin Dawakin-Kudu da Warawa a Majalisar Tarayya dake Abuja.

Ko ma mene, ga dukkan alamu APCn Kano tana neman yiwa kanta fafalolo a 2027 yayin da jam’iyyar NDC ke cigaba da karfafa karfi da tasiri a zukatan al’ummar jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here