Daga Hassan R Jibrin
Dan takarar majalissar dokokin jihar Kano daga Karamar Hukumar Dawakin-Kudu, Hon Adamu Sani Gano, ya jaddada kudurin sa na baiwa ilimi fifiko kamar yadda madugun darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Kwankwaso ke nuna wa, da zarar ya lashe zaben 2027.
Dan takarar ya fito ne daga yankin mazabar Gano a jam’iyyar NDC.
Ya bayyana hakan ne, jim kadan bayan mika takardar sha’awar takarar sa ga shugaban jam’iyyar NDC, Hon Yusuf Dan bagina a ofishin sa dake rukunin gidajen Kwankwasiyya.
“Harkar Ilimi, noma, lafiya, wasanni da kula da mata da yara kanana, musamman marayu suna daga cikin muradun wannan fitowa da kuma bada cikakiyar goyon baya ga Gwamnati domin aiwatarwa” acewar sa.
Ya Kuna ja hankalan ‘yan-uwansa matasa, da su tabbata sun mallaki katin zabe domin cikar burin ganin bunkasuwar tattalin arziki da kwanciyar hankali.
Samun sauyi a siyasar 2027, ganin yanzu matasa sun farka daga barcin da wasu dattawa a fagen suka sa su, wata manuniya ce ta mai laya ya kiyayi mai zamani.










