Naziru Hamisu.

Jam’iyyar ADC ta fito da wani sabon tsarin rabon mulki da nufin tabbatar da haɗin kai a tsakanin ‘yan adawa kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yayin da ake fargabar cewa takaddama tsakanin masu neman takara na iya janyo rabuwar kai bayan zaɓen fidda gwani.

Shirin da jam’iyyar ta gabatar na neman daidaita muradun masu ruwa da tsaki ne, domin hana ɓarkewar rikici bayan kammala zaɓen cikin gida, tare da ƙarfafa haɗin kai da tsari mai dorewa a cikin tafiyar siyasar ‘yan adawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here