Daga Hassan R Jibrin.

Wani jigo a jam’iyyar ADCn Karamar Hukumar Dawakin-Kudu dake jihar Kano, Mallam Mika’il Gidan-Kuka, ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar ADC a fadin Najeriya, da su kai zuciya nesa dangane da hukuncin da Hukumar Zaben Najeriya ta dauka wajen soke shugabancin Sanata Davif Mark.

Acewar jigon irin wannan danyen hukunci, babu alheri sai dai tada zaune tsaye a siyasa da zaman lafiyar Kasar. “Idan tururuwa taso lalacewa, sai ta fara fuffuke” inji Mallam Mika’il.

Idan za’a iya tunawa, a kwanakin baya ne Hukumar Zaben ta NEC, ta soke sunayen shugabanin ADC bisa dogaro da wata takardar umarnin Kotu me cike da sarkakiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here