Naziru Hamisu.
Shugaban matasan jam’iyyar adawa ta ADC ɓangaren Nafiu Bala Gombe, Hon. Sultan Ahmed Bello ya sanar da ajiye muƙaminsa.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Hon. Sultan ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda yake fuskantar barazana da kuma shan tsinuwa da munanan addu’o’i daga wajen al’umma saboda abin da ya ke faruwa da kuma goyon bayan Nafiu Bala da ya ke yi.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.










