Daga Sale Hussaini Takai

A baya-bayan nan ne ƴansanda suka tsare wata matashiya mai suna Tititlayo Ibrahim, ƴar jihar Ondo kan laifin da ba ta san komai a kai ba bayan sayan layin waya da aka taɓa amfani da shi.Duk da cewa ba ta aikata laifi ba, ƴansanda sun bibiyi layin waya da masu garkuwa suka taɓa amfani da shi da ke hannunta wajen tsare ta. Masana shari’a sun kwatanta wannan lamari da rashin adalci, inda suka buƙaci matashiyar ta dangana da kotu don neman hakkinta.Yayin da take tattaunawa da BBC, Titilayo ta bayyana abin da ta fuskanta a hannun ƴansanda kan abin da ta san komai a kai ba.Lamarin ya faru ne a Akure, babban birnin jihar Ondo.Titilayo ta tuna yadda wata mata ta kira ta a waya inda take cewa tana son sayan wani abu a wurinta. A ce ba ta sani ba ƴansanda ne ke son kama ta ba.”Lamarin ya afku ranar 16 ga watan Oktoban, 2025, lokacin da wata bakuwar lamba ta aika sako ga layin da nake amfani da shi wajen yin kasuwanci.”Ta buaci na aika hotunan abin da nake sayarwa, sai na aika, inda ta zaɓi biyu daga cikin kayayyakin.”Ta ce wayarta ta samu matsala tana amfani ne da wayar mijinta. Don haka ta kai musu kayan wajen da suke jira don karɓar kuɗinta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here