Daga Hassan R. Jibrin.
Shugaban Kungiyar Arewa APC, Alhaji Saleh Zazzaga, ya sanar da janye wa’adin sati biyu da kungiyar ta baiwa Shugaban jam’iyyar APC na kasa Farfesa Nantawe kan sauka daga shugabancin jam’iyyar.
Alhaji Saleh Zazzaga, ya ce wancan wa’adin bisa kuskure ne kungiyar ta bayar.A wata sanarwa da ya fitar, ya kuma roki gafarar shugaban jam’iyya da ita kanta APC A cewarsa burin Kungiyar ne taga APC an samu cikakken hadin kaigabannin zaben 2027, amma ba rarrabuwa ba.
Kwanakin baya ne Kungiyar ta zargi shugaban jam’iyyar da rashin iya gudanar da lamuran ‘yan takarkari ta nuna banbanci a tsakinin ‘ya’yan jam’iyyar ta APC da kuma tatsar makudan kudade daga garesu.










