Daga Hassan R. Jibrin.
Sanatan Kano ta Tsakiya kuma mataimakin Shugaban Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawa bangaren marassa rinjaye, Sanata Rufa’i Hanga, ya tabbatar da cewar bisa yardarsa Dr Nasiru Gawuna, ya samu tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Sanata Hanga, ya kara da cewa, sadaukar da wannan dama yayi tane domin karfafa cigaban jam’iyyar NDC da kuma girmama jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
“Ita Kwankwasiyya tsari ne na sadaukar da bukatunka domin karfafa amana, zan ci gaba da bayar da cikakken goyon baya domin samun duk wata nasara ga jam’iyyar NDC daga sama har kasa”.
A cewar Sanata HangaTataburza da ta nemi kai Kwankwaso shiga wani wadi kan kokarin sulhuntawa a tsakanin tsohon mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Abdussalam Gwarzo da Dr Nasiru Gawuna kan wadda zai yi takarar kujerar Gwamna, ta kai da saura kiris da yin zaben fidda gwani, amma daga baya, Gawuna ya amince da tayin kujerar Sanata Rufa’i Hanga.










