Daga garin da ke kan tudu wanda shi ne mafi tsawo da ke kan Tudu a cikin biranen Najeriya, kuma yanki mai tsaunuka da gangara masu yawam
Gari ne da yake da kimanin mita dubu daya da dari shida (1,600) zuwa dubu daya da dari takwas (1,800) sama da matakin teku.
Yanayin garin yana da sanyi sosai idan aka kwatanta da sauran sassan Najeriya, wasu lokuta yanayin yana iya sauka ƙasa da ma’aunin Celsius 15, musamman da safe da dare, wannan ne ya sa mutane da dama ke cewa garin “tamkar Turai” ne a Najeriya.
Wannan bayanin zai iya sa mafi yawan mutane su gane wannan wani gari ne, la’akari da kasancewar garin na musamman.






