Daga Hassan R Jibrin.

Rahotanni dake fitowa daga jihar Edo a kuduncin Najeriya, sun tabbatar da cewa Hukumar Yaki da Sha da Hana Fataucin Kwayoyi ta NDLEA, ta samu nasarar kwato mugayen kwayoyi da yawan su yakai nauyin tan 5.7, tare da cafke mutune 166.

Kwamandan Hukunar dake jihar ta Edo Mr Micheal Ofoyeju, ya shaidawa manema labarai yayin bitar nasarorin da Hukumar ke samu a jihar.

A farkon shekara nan, mutane 46 da kwayoyi masu nauyin kilogiram 2,375.5298 aka kama, yayin da a watan Fabrairu mutane 56 da kwaya mai nauyin kilogiram 900.8939.

A watan Maris, shi aka fi damkar mutane har 64 da kwayoyi masu nauyin kilogiram 2.,467.6781Rundunar, acewar Mr Micheal Ofuyeju, mutane 7 ne Kotu ta yankewa hukuncin daurin rai-rai a gidan gyaran hali daga cikin shari’o’i 105 da Hukumar ta gabatarwa Kotuna tun daga farkon shekarar nan kawo yanzu.

Jihar ta Edo, duba da yawan surkukiyar dazuzzuka dake a cikinta, hakan yana taimakawa wajen noman ganyen tabar ta wiwi da sauran ire-iren ciyayi dake samar da abubuwan sa maye.

Tuni dai Hukunar karkashin jagorancin Birgediya Buba Marwa (Mai Ritaya), ta kudiri ganin bayan fatauci da tu’ammali da kwaya a fadin Kasar, amma wannan buri da fatan ka iya dusashewa ganin yadda Kotuna ke jan kafa wajen gudanar da shari’o’in masu nasaba da laifukan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here