Daga Alhaji Musa Muhammad Hadejia
Kungiyar Cigaban Matasan Garin Kaugama sun yaba da salon takon Mulki na shugaban karamar hukumar Kaugama Usman Masaki Dansule.
Shugaban kungiyar Tasi’u Garba Kaugama ya sanar da haka ga jami’in yada labarai na karamar hukumar Kaugama Musa Muhammad Hadejia.
Shugaban yace shugaban karamar hukumar Usman Masaki ya sayo Na’urorun Samar da hasken Rana domin yin anfani da su wajen Samar da wadataccen ruwan Sha a cikin Garin Kaugama da kewaye.
Yace kungiyar tana Gudanar aiyukan Gyaran ruwan Sha a yankin domin bada gudun mawa don ganin al’ummah sun tallafawa aiyukan Gwamnati domin moriyarar al’ummar yankin.
A jawabin sa ta Hannun Sakataren karamar hukumar Kaugama Garba Musa Kaugama yace karamar hukumar a shirye take wajen aiwatar aiyukan Raya kasa domin moriyar al’ummah.










