Daga Hassan R Jibrin.
Shugaban jam’iyyar PRP na kasa Dr. Hakeem Baba Ahmed, a wata hira da gidan talabijin na Arise, ya bayyana cewa; makusantan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne suka hana masa masaniyar gaskiyar lamuran dake faruwa a kasa, saboda rashin iya gudanar da mulki.
“Yunwa, fatara da rashin tsaro sune tukuicin ‘yan Najeriya daga wannan mulkin” acewar Dr. Baba Ahmed.
A wata sabuwar kuma, Sakataren Yada Labaran jam’iyyar ADC, Mallam Bolaji Abdullahi, yayi fatali da wasu rahotanni dake yawo a kafafen sadarwa cewar suna taba alli da PRP domin Zama wukar gindi a zaben 2027.
“Ba ma tattaunawa da kowacce jam’iyyar akan shari’ar mu ko kuma abin da ya shafi 2027” Inji Mallam Bolaji.










