Kungiyar Matasan Cigaban Garin Kaugama ta Gudanar da Gyaran Lalatattun Tashar Samar da ruwan Sha a fadin yankin.
Daga Musa Muhammad Hadejia.
Kungiyar Matasan cigaban Garin Kaugama ta Gudanar da aiyukan raya kasa a cikin Garin Kaugama domin inganta rayuwar al’ummah.
Shugaban kungiyar Matasan cigaban Garin Kaugama, Tasi’u Garba ya sanar da haka yayin Gudanar da aiyukan Gyare-Gyaren Fanfunan Samar da ruwan Sha acikin Garin.Shugaban yace kungiyar tana inganta lafiyar al’ummar yankin ne ta Hannun tattara gudun mawa da matasa, dattijai da Kuma attajirai yankin suke bayarwa.
Sakataren Kungiyar cigaban Matasan cigaban Garin Kaugama, Musa Yusuf Adamu yace kungiyar ta Gudanar aiyuka wajen gyara tashar Samar da ruwan Sha Mai anfani da hasken Rana a Unguwar Kara, sashen ilmi, da sauran su domin moriyarar al’ummar yankin.
Tun da farko dai shugaban kungiyar Tasi’u Garba Kaugama yace kungiyar tana tallafawa Matasa masu sha’awar shiga aikin Damara da Kuma tallafawa karatun Matasa domin samun ingantacciyar rayuwa.










