Daga Hassan R. Jibrin.
Hukumar dake kula da Dabbobin daji ta Kenya (KWS) ta sanar da jajircewa wajen gano hakikanin abin da yayi sanadiyyar mutuwar giwaye goma sha shida a gandun dajin Amboseli-Kinama, makwanni shida da suka wuce, wato daga 24 ga watan Yuni zuwa 31ga watan Yuli na wannan shekarar.
Binciken farko da aka gudanar a Jami’ar Nairobi ya nunar da cewa, giwayen sun mutu ne ta dalilin ciyar da su gubar “cyanide”, wacce ta janyo shanyewar bangaren jiki, daga barin kafafuwansu na baya inda yafi shafarmanyan mata da kanana giwayen wajen mace-macen.
Babban Darekta a Hukumar ta KWS, Mr Erectus Konga, ya bada tabbacin ga al’ummar Amboseli-Kinami da masu yawon bude idanu dake zuwa gandun dajin, bayar da cikakkun bayanai kan mutuwar dabbobin.
Shi dai wannan gandun dajin na Amboseli National Park, kawo yanzu hukuma ba ta rufe shi ba










