DAGA: MUHAMMAD CHAMAMA.
Almajirai guda huɗu sun rasa rayukansu a Kano bayan cin kifin da ake zargin yana ɗauke da gubar maganin bera.
Lamarin ya faru ne a yankin Kadage Sharifai, a Ƙaramar Hukumar Ungogo, inda mamatan suka kasance almajirai a Tsangayar Malam Iliyasu Mai Tsangaya.
Sanarwar da Shugaban kungiyar Tsangaya Media Network Sani Musa Nuhu ya fitar ta ce, bayan almajiran sun ci kifin sai suka kamu da matsanancin rashin lafiya, lamarin da yasa aka garzaya da su Asibitin Malam Aminu Kano amma daga bisani huɗun suka rasu a daren Lahadi.
Tuni dai aka gudanar da jana’izar mamatan bayan samun umarni daga Dagacin yankin da kuma DPO.










