Hassan Turaki.
Kotun Ƙoli ta Ƙasar Saudiyya ta buƙaci al’ummar Musulmi a duk faɗin ƙasar su duba jinjirin watan Shawwal a ranar Laraba, 18 ga Maris, 2026.
Sanarwar ta ce Ganin jinjirin watan ne zai tabbatar da ranar Eid al-Fitr. Idan aka ga jinjirin watan a wannan yamma, za a yi Sallar Idi a ranar 19 ga Maris.
Amma idan ba a gan shi ba, za a cika kwanaki 30 na watan Ramadan, sannan a yi Idi a ranar 20 ga Maris.










