Hassan Turaki.

Shugaban Karamar hukumar Kaugama ya haske mazabar Danbuwaran.Daga Nusa Muhammad Hadejia.

A Cigaba da ingnanta kayayyakin more rayuwa din inganta rayuwar al’ummar karamar hukumar Kaugama.Shugaban karamar hukumar Kaugama Usman Masaki Dansule ya bada umarnin gyaran Na’urar rarraba Samar wutar lantarki a garin Dusare dake Mazabar Dabuwaran.

Hakan ya biyo bayan lalacewa sa Na’urar tayi wadda aikin gyaran na daf da kammala .A jawabin sa shugaban karamar hukumar Kaugama Usman Masaki Dansule ya lashi tokobin gyaran ababen more rayuwa da suka samu matsala a fadin karamar hukumar ta Kaugama.

Wasu daga cikin al’ummar sun nuna farin cikin su da godiyar su wajen gyara musu Na’urar rarraba wutar lantarki domin inganta rayuwar su dakuma inganta tsaro a fadin yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here