Daga Hassan R Jibrin.

Maigirma Gwamnan jihar Jigawa, Mal. Umar Namadi ya kai ziyarar ta’aziyya ga Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Abubakar Sayyadi Mahmud Usman CON dangane da hatsarin Kwale-Kwale da ya faru a kauyen Malamawar ‘Yandutse dake Karamar Hukumar Ringim.

A lokacin ziyarar ne,Gwamnan yayi addu’ar ALLAH ya karbi shahadar mamatan, ya kuma baiwa masarautar da iyalai hakurin wannan babban rashi daya shafi ilahirin jihar.A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin, a madadin masarautar da iyalan mamatan, yayi godiya mai yawa ga gwamna kan wannan kulawa, inda yazo da kansa ba tare da wakilci ba.

Idan dai ba’a manta ba a jiya lahadi ne aka samu mummunan iftila’in kifewar wani kwale-Kwale dake dauke da mutane arba’in a kauyen Malamawar ‘Yandutse wadanda aka sarin su yara kanana ne.

Hakan ya janyo rashin rayuka akalla 15 da bacewar Wasu da dama yayin da aka shiga jimami a fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here