Daga Hassan R Jibril.
Na’ibin masallacin Jami’u Sheik Abdul Kadir Jelani dake garin Gano, a Karamar Hukumar Dawakin-Kudu a jihar Kano, Sheik Al-Bashir bn Ilyas bn Abbass, ya bukaci al’ummar musulmaiI da su zamo masu tausayawa junansu da kuma sauran al’umma.
Rokon yana kunshe ne a wani jawabi da ya gabartar, alokacin taron fadakar da al’umma kan falalar goman karshe na watan Ramadan a unguwar Alkalawa a garin Gano.
A inda ya kara jawo hankulan musulmai da zama tsintsiya madaurinki daya, kamar yadda Allah ya umarta kan kaucewar rarrabuwar kawuna.
Mabiya dariku mabanbanta ne suka halarci taron, a inda daya daga cikin wadanda suka shirya, Mallam Nura Muhammad Dauda, ya nuna farin ciki dangane da amsa gayyatar ba tare da nuna banbance- banbancen darika ba.
Ya kuma nuna karfin gwuiwar sake tsara irin wannan taron a wani lokaci anan gaba.
An kammala taron ne da addu’o’in samun zaman lafiya a Najeriya da kasashen Gabas ta Tsakiya da kuma sauran sassan duniyar musulmaiI.










