Daga Hassan R. Jibrin.
Mamakon ruwan sama a garin Igarra dake Karamar Hukumar Akoko-Edo a jihar Edo, yayi sanadiyyar rushe gidaje fiye da 20, yayin da mutum guda ya rasa ransa.
Ambaliyar ruwan ta lalata makabartu da dama a garin na Igarra. Wuraren da abin ya fi tsananta sun hada titunan Pope Francis, lungun Iretutu, Market Road , Okpe Road, da kuma Rest House Road.
Wasu gidaje dake kusa da Ofishin ‘Yan sandan yankin da na tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar karkashin Chief Obaseki sun samu mummunar lalacewa.
Ganau sun tabbatar da cewar mamakon ruwan ya shafe awanni da dama kafin daukewar sa.










