Daga Hassan R. Jibrin.

An samu rahotanni dake tabbatar da faruwar wani hatsarin kifewar Kwale-Kwale mai dauke da yara kanana da manya kimanin mutane 40 daga garin Malamawa zuwa ‘Yan Dutse, a Karamar Hukumar Ringim dake Jihar Jigawa.

Fadar Mai Martaba Sarkin Ringim ta mika sakon gaisuwar ta’aziyyar ga Shugaban Karamar Hukumar da kuma iyalan mamatan.Manyan masu rike da mukaman gargajiya da wasu Hakimai na daga cikin tawagar Masarautar, wajen kai ziyarar ga iyalan mamatan.

Masu fashin baki na ganin samarwa ire-iren wadannan al’ummomi Kwale-Kwale na zamani zai rage afkuwar hadararruka yayin gudanar da zirga-zurgar yau da kullum akan kogunan yankunan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here