Daga Wakilin Mu.
Tarihin Marigayi Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim.An haifi Galadiman Kano, Alhaji Ahmadu Tijjani Hashim, ɗan Turakin Kano Hashimu, ɗan Sarkin Kano Abbas, ɗan Sarkin Kano Abdullahi I, ɗan Sarkin Kano Ibrahim Dabo, a shekarar 1932 a garin kiru Kano.
Ya fara karatun firamare a garin Bebeji a shekarar 1944. Daga nan ya shiga Kano Middle School, inda ya yi karatu har zuwa shekarar 1951.
A shekarar 1952, ya fara aiki a Hukumar Lafiyar Dabbobi ta Kano a matsayin malamin dabbobi da mai kula da tsaftar dabbobin da ake yanka a mayanka.
A shekarar 1956, aka zaɓe shi ɗan majalisar dokokin Arewacin Najeriya mai wakiltar Sumaila.
A lokacin da yake majalisa, ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da Shugaban Hukumar Ba da Kwangila ta Kaduna.
Shugaban kwamitin tabbatar da nasarar jam’iyyar NPC a Lardin Sardauna.Ministan Harkokin Cikin Gida na Jihar Arewa.
Kwamishinan Lardin Kabba, kafin juyin mulkin soja ya kawo ƙarshen gwamnatin farar hula.
Bayan dawowarsa Kano, marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya naɗa shi Dan Isan Kano, tare da ba shi matsayin kansila mai kula da ayyukan gayya da taimakon kai da kai.
A shekarar 1976, ya samu ƙarin girma zuwa sarautar Turakin Kano, inda aka ba shi kula da Gundumar Kumbotso.
A shekarar 1980, ya zama kansila ba tare da ofis ba saboda yawan ayyukansa. A shekarar 1989, aka ɗaga shi zuwa sarautar Dan Iyan Kano, tare da ci gaba da kasancewa kansila ba tare da ofis ba.
A shekarar 1992, aka naɗa shi Galadiman Kano, ɗaya daga cikin manyan sarautun Kano, kuma shugaban kwamitin kuɗi na Majalisar Sarki. A shekarar 2012, Mai Martaba Sarkin Kano ya ƙara masa aikin Hakimin Birnin Kano, wanda ya ci gaba da gudanarwa har Allah Ya karɓi rayuwarsa.
Marigayi Alhaji Tijjani Hashim ya yi suna da adalci, tausayi, karamci da taimakon jama’a. Ya kasance mutum mai buɗaɗɗen ƙofa, wanda kowa zai iya zuwa wajensa ba tare da tsoro ko shakka ba.
Rasuwarsa ta jawo alhini a tsakanin al’umma, domin ya kasance mai sauraron koke-koken jama’a, mai sasanta mutane, kuma mai taimaka wa matasa wajen samun aikin yi da dogaro da kai.
Haka kuma, ya kasance mutum mai sauƙin kai, mai tawali’u, wanda bai nuna bambanci tsakanin mutane ba. A fagen siyasa kuwa, ya taka muhimmiyar rawa tun daga zamanin Majalisar Dokokin Arewacin Najeriya a zamanin Sardaunan Sokoto, inda ya yi aiki a matsayin sakataren majalisa.
Jagoranci da shawarwarinsa sun taimaka wajen gina fitattun ‘yan siyasa da dama a Najeriya. Duk da kasancewarsa basarake, ya kasance abin girmamawa ga ‘yan siyasa da sauran shugabanni, waɗanda ke neman shawararsa da gudummawarsa wajen tafiyar da al’amuran ƙasa.
Allah Ya jiƙan Marigayi Alhaji Tijjani Hashim (Galadiman Kano), Ya gafarta masa, Ya yalwata kabarinsa, Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa. Amin.










