Daga Hassan R Jibrin

Mai Martaba Sarkin Ringim, Dr Abubakar Sayyadi Mahmoud Usman CON, ya umarci al’ummar masarautar da a koma da Allah domin neman afuwarsa.

A wata sanarwa a shafin masarautar na Facebook, ya janyo hankalin al’umma da rashin samun ishesshen ruwan sama sabanin a wasu wurare daban-daban.

Umarnin ya hadar da yawan dukufa wajen mika duk wasu lamura ga Ubangiji tayin addu’o’i a gidaje, masallatai da sauran wuraren taron jama’a.

Ganin har yanzu ana cikin halin karancin ruwan sama a mafi yawancin masarautar ya zamowa fadar Sarkin damuwa, ta sa bayar da umarnin domin karin kusantar Ubanciji don neman dauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here