Hassan Turaki.

Babban limamin jumma’a, Malam Muktar Abubakar wanda akafi sani da Malam Babba, ya yi kira ga al’umma da su ji tsoron Allah hakikanin tsoro, domin Shi ne kadai mai canza dukkan halin rayuwa yadda ya ga dama.

A cikin hudubar Juma’a, Malam Babba ya ce Allah ne ya cika duniya da abubuwa, kuma zai dauke su har wata rana za a wayi gari babu komai a duniya. Ya tuna da cewa Manzon Allah S.A.W ya bayyana cewa an halicci rayuwa da mutuwa ne don su zama darasi ga dan Adam.

“Yau kana cikin farin ciki, gobe kana cikin bakin ciki. Yau ana daukaka ka, gobe ana dusar da lamuranka. Duk daga Allah ne, don haka mu koma gare Shi,” in ji shi.

Malam ya ja hankalin shugabanni game da takama da girman kai na mulki. Ya ba da misali da shugaban kasar Italiya da ya taba cika baki yana cewa ya fi karfin kowa, sai gashi cikin awa kadan cutar COVID-19 ta sa ya fito yana kuka. Ya ce duk girman kowa, zai iya rasa mulki a duk lokaci.

Haka zalika limamin ya bayyana damuwa kan lalacewar tarbiyya, musamman yadda wasu mata ke hawan babur guda biyu suna zama na rashin kunya. Ya bayyana hakan a matsayin masifa da ke lalata tarbiyyar al’umma.

Ya kuma yi Allah wadai da al’adar daukar hotuna da bidiyoyin batsa da maza da mata ke tura wa juna ta waya, inda ya ce suna kara jawo bala’i. Ya ba da shawara cewa mumini idan ya ga haka ya kau da kai ya shagala da addu’a.

Malam Babba ya kammala da kira ga al’umma da su dawo ga Allah, su rike kyawawan dabi’u domin samun zaman lafiya da cigaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here