ABDULLAHI AMINU JAHUN.

An bukaci al’umar musulmi da su nemi kusanci da Allahu S.W.T da yin layya tare da sanya kwadayin samun lada a cikinta da kuma kyautata layyar domin samun kubuta a ranar Alkiyama.

Na’ibin Limamin Babban Masallacin Juma’a na cikin Garin Jahun, Khalifa Malam Muhammad Adamu ne ya yi kiran yayin da yake gabatar da kudubar sallar idi babba a Masallacin Idi dake Yakudima daura da Makarantar Kimiyya ta ‘yan mata dake Jahun a ranar Laraba.

Ya ce a wannan rana ta Hajji babba akwai alamomin addini da suke bayyana kuma a wannan ranar ce ake yin koyi da sunnar Annabi Ibrahim A.S. ta yin layya wacce babbar Ibadah ce da ake samun lada mai dinbin yawa a cikinta.

Na’ibin ya ce a wannan rana ce Allah SWT ya jarrabi Annabi Ibrahim A.S. da yanka dansa Annabi Isma’il A.S wanda da haka ne layya ta zama wajibi a mazahabar Abu Hanifa matukar mutum ya mallaki nisabin Zakka, yayin da layya ta zama Sunna a sauran mazahabobi guda uku.

Khalifa Malam Adamu ya ce a wannan babbar rana duk wani bawa da zai yi aikin alkhairi Allah SWT zai ninka masa ayyukan sa na lada, kazalika ana nunkawa bawa da duk wasu ayyukan sa na sabon da ya aikata.

Khalifa Malam Muhammad Adamu ya kuma yi kira ga wadanda suka samu damar yin layyar da su taimakawa marasa karfi da sadaka, su kuma bada kyauta ga makusantan su sannan su gabatar da wani kason na layyar ga kawunan su.

Ya kuma yi adu’ar Allah ya karbi Ibadunmu ya kare mu daga dukkan sharri ya datar da mu duniya da lahira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here