Daga Hassan R Jibrin.

Babban limamin Gano dake Karamar Hukumar Dawakin-Kudu a jihar Kano, Sheik Umar Yusuf Gidan Digawa, kuma Shugaban Kwamatin Shura, a sakon da ya wallafa ta kafar sada zumunta ga dokacin musulmai, ya shawarci musulmai da yin azumin ranar Arfa.

Shehun malamin ya kwatanta falalar dake cikin ibadar baya ga gafarar Allah ga masu yi da kuma wasu sauran ni’imomin dake tattare a ciki.Sakon wani maimaici ne ga hudubarsa ta ranar Juma’a da ta gabata.

Ya kuma yi amfani da damar wajen kara kiran iyaye da a zage damtse akan tarbiyyar yara wadanda ake sa ran sune shuwagabannin gobe.

Ya kuma bukaci mahukunta da sauran al’umma da sanin cewar, masu kiwo ne kuma Allah zai tambayi kowa yadda ya gudanar da amanar da aka bashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here