Daga Hassan R. Jibrin.


Yayin da guguwar neman takara ke kadawa a cikin zukatan wasu ‘yan siyasa masu ci da sabbin shiga.
Kwamatin tantance masu zawarcin kujerun a bangaren majalisun tarayya, na jam’iyyar APC sun wayi gari da abin al’ajabi maikama da tatsuniya ko wasan kwaikwayo irin na sinima, a inda Honarabul Muhammed Sadis Buba ( Al’ajabin Sarkin Zazzau),ya girgiza kwamatin na APC.Kasancewarsa wada mai muryar yara masu shekaru 16 zuwa 29.
Kamar yadda ya shaidawa kwamatin shekarunsa 30 da haihuwa, kuma ‘yan mazabarsa ta Sabon Garin Zariya a jihar Kaduns suka bukace shi da yin takarar domin wakilinsu ya gaza sauke nauyi.
Takarar ta sa, ta bude wani sabon babi a siyasar Najeriya ta baiwa masu bukata ta musamman damar shiga harkokin siyasa da mulki
Duba da irin halittar sa wasu na ganin idan har ya samu nasarar a zaben 2027, dole a samar masa. da kujerar ta musamman sabanin kujerun da ke cikin zauren majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here