Ibrahim A Makama.
Jamʼiyyar NDC ta buƙaci matan Jihar Kano su fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 ta hanyar yin rajistar katin zaɓe da kuma shiga jam’iyyar domin su taka rawar gani wajen zaɓen shugabanni.wannan na cikin sanarwar da Shugabar Matan NDC ta Jihar Kano, Hajiya Farida Sani Kamba, ta fitar.Sanarwar ta yi kira ga mata da kada su bari a yi amfani da kuɗi wajen siyan ra’ayinsu, tana mai cewa ƙuri’arsu muhimmiyar hanya ce ta zaɓar shugabannin da za su inganta rayuwarsu da ta iyalansu.Kamba ta kuma buƙaci matan da su tabbatar sun yi rajistar a Katin Zaɓe tare da shiga jamʼiyyar NDCn domin su samu damar taka rawa a harkokin siyasa.Sanarwar ta bayyana cewa NDC na da tsare-tsaren inganta rayuwar mata ta fuskar ilimi, kiwon lafiya, tattalin arziki da ƙarfafa musu gwiwa domin su taka rawa a ci gaban al’umma.










