Daga Hassan R Jibrin.
Majalisar Matasan Arewa sun bukaci majalisun dokokin Enugu da Ogun da su fara shirye-shiryen tsige gwamnoninsu.Bukatar ta biyo bayan wata tirka-tirka da ta shiga cikin kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, a inda wasu mambobin ashitin suka bayyana sauke shugabansu kums gwamnan jihar Imo Hope Uzodumma da mataimakinsa Uba Sani na Kaduna.Sakataren Majalisar Matasan na Arewa, Muhammad Sanni, ya sanar da bukatar akan nuna zargin gwamna Dapo Abiodun da Peter Mbah da yiwa takarar Shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu nakasu a kakar zabe mai zuwa.Wasu gwamnonin APCn, a taronsu da suka gudanar, sun jaddada goyon bayan Hope Uzodumma da Uba Sani.Idan APC ba ta yi kokarin dinke barakar ba, za ta iya tsintar larabarta a talata a jihohin da suke goyon bayan Dapo Abiodun da Peter Mbah.










