Daga Hassan R. Jibrin.
Allah ya yiwa babban limamin Okotonwa dake Kogi ta kudu,a jihar Kogi rasu.
Sheik Pa Ochelifu Dan asalin kabilar ibo ne. Ya kuma shafe shekaru da dama yana koyar da karatu da kuma addinin musulinci a tsakanin kabilarsa.
Dawowar sa garin na Okotonwa, ya zamo babban limamin garin da kuma cigaba da da’awar.
ALLAH yayi masa rasuwa bayan shafe shekaru da yawa ba kasafai yake iya fitowa ba dalilin tsufa Allah ya jikan Sheik Ochalefu Onucheyo.










