Daga Hassan R Jibrin.
Wasu fusatattun matasa a unguwar Sabuwar Panteka dake cikin garin Kaduna sun zamo alkalan kansu.
Hakan ya faru ne, bayan wata motar dakon mai tayi hatsari a kan titin Kaduna Bye-pass, inda tayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.
‘Yan tijaran matasan sun bankawa motar wuta. Kawo yanzu jami’an tsaro ba su kai da cika hannayen su da wadannan matasan ba, amma an Fara gudanar da bincike dangane da faruwar lamarin.










