Hassan Turaki.

Kwamishinan Ayyuka na Musamman da Raya Karkara na Jihar Bauchi, Farouk Mustapha, ya ajiye mukamin sa domin Shiga Takara A zaɓen 2027.

Rahotanni sun tabbatar da cewa murabus ɗin na daga cikin shirye-shiryen sa na neman wani muhimmin matsayi a zaɓen da ke tafe, lamarin da ke ƙara zafafa fafatawar siyasa a jihar Bauchi.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin da dama daga cikin masu rike da mukaman gwamnati ke barin kujerunsu domin bin ka’idojin zaɓe tare da shiga fafatawar neman mukamai daban-daban.

Ko da yake har yanzu ba a bayyana takamaiman kujerar da zai nema ba, ana sa ran zai fito fili nan gaba domin sanar da mabiyansa da al’umma gaba ɗaya kan burinsa da tsare-tsarensa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here