EDITA.
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta samu nasarar lashe rumfar zaɓe ta farko a zaɓen gwamnan jihar Ekiti da ke gudana a halin yanzu.ADC ta yi nasara ne a rumfar zaɓe da ke Ajagbala Hall, a yankin Okeruku Ward 02 na ƙaramar hukumar Ikere.
Sakamakon da wakilinmu ya gani ya nuna cewa ADC ta samu ƙuri’u 39, yayin da jam’iyyar APC ta zo ta biyu da ƙuri’u 29.
Ita kuwa jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 17, inda ta kasance ta uku a wannan rumfar zaɓe.
A baya dai ɗan takarar ADC, Dare Bejide, ya bayyana damuwarsa kan zargin cin zarafi da tashin hankali da ya ce an yi wa wasu daga cikin magoya bayansa.
A halin yanzu, sakamakon wasu rumfunan zaɓe daban-daban na ci gaba da fitowa yayin da ake tattara sakamakon zaɓen daga sassan jihar.










